Tsallaka zuwa babban shafi

Kuɗaɗe masu cin gashin kansu (DeFi)

  • Yanayin da zai canza kasuwar hada hadar kuɗaɗe a duk faɗin duniya.
  • Samfuran da ke ba ku damar yin aro, ajiya, zuba jari, kasuwanci, da sauran su.
  • Bisa yadda kowa zai iya tsarawa a buɗaɗɗiyar hanyar fasaha.

DeFi buɗaɗɗen tsarin kuɗi ne na duniya wanda aka gina don zamanin intanet - madadin tsarin da ba shi da kyau, sarrafa shi sosai, kuma ana gudanar da shi ta hanyar ababen more rayuwa da matakai na shekaru da yawa. Yana ba ku ikon sarrafawa da kuma ganin kuɗin yanayin ku. Yana ba ku damar ganewa har zuwa kasuwannin duniya da madadin kuɗin gida ko zaɓukan banki. Kayayyakin DeFi suna buɗe sabis na kuɗi ga duk wanda ke da haɗin Intanet kuma masu asusu da su galibi mallakar su ne. Ya zuwa yanzu dubun-dubatar biliyoyin daloli na kiripto ya gudana ta aikace-aikacen DeFi kuma yana haɓaka kowace rana.

Me DeFi?

DeFi gamayya ta kalma ce don lissafin da sabis da ke ba da iso da damar duk wanda zai iya amfani da Ethereum - duk wanda ke da ke da asusun. Tare da DeFi, kasuwanni a koyaushe a buɗe suke kuma babu hukumomi na tsakiya waɗanda za su iya toshe biyan kuɗi ko hana ku damar yin amfani da komai. Sabis ɗin waɗanda a baya suna jinkiri kuma suna cikin haɗarin kuskuren ɗan adam sun kasance ta atomatik kuma sun fi aminci yanzu cewa ana sarrafa su ta lambar da kowa zai iya dubawa da bincikawa.

Akawai bunkasar arzikin kiropto da ke can waje, inda za ku iya ba da rance, aro, dogo/gajere, samun riba, da sauran su. Mafi sanin-kiriptoa kasan Argentina sun yi amfani da DeFi don tserewa daga hauhawar farashin kaya. Kamfanoni sun fara ɗaura wa ma’aikata albashin su a ainihin lokaci. Wasu mutane ma sun cire da kuma biya lamuni na miliyoyin dala ba tare da bukatar bayanan sirri ba.

DeFi da hada-hadar kuɗi na gida

Ɗaya daga cikin hanyoyin ganin iyaƙar DeFi don fahimtar matsalolin da ke faruwa a yanzu.

  • Wasu mutanen ba a basu damar saita asusun banki ba ko kuma amfani da sabis na kuɗi.
  • Rashin wadatacciyar sabis na kuɗi na iya hana mutane a ɗauke su aiki.
  • Sabis na kuɗi na iya hana a biya ku kuɗi.
  • Kuɗin da za a cire na ɓoye daga sabis na hada-hadar kuɗi daga jikinku ne.
  • Gwamnati da kuma jami'o'i sanannu na iya kulle kasuwanni idan suka gadama.
  • Awannin ciniki a koyaushe ana iyaƙanta su zuwa awannin kasuwanci na kowane yanayin lokacin yanki.
  • Aika kuɗi na iya jimawa saboda tsarin ɗan'adam.
  • Akwai babban tsarin sabis na kuɗi da ake biya saboda jami'o'in da ke tysakani suna buƙatar rabon su.

Kwatantawa

DeFiAyyukan kuɗi na gida
Ku rike kuɗin ku.Kamfanoni na riƙe da kudin ku.
Ku na da iko akan inda kuɗin zai tafi da kuma yadda zaku kashe su.Dole ku yadda da kamfanoni kar su yi amfani da kuɗin ku yadda bai dace ba, kamar ba da rance ga masu karɓar bashi da hadari sosai.
Turawa yana faruwa a cikin mintoci.Biyan kuɗi na iya ɗaukan kwanaki saboda hanyoyin sarrafa shi.
Ayyukan hada-hadar kuɗi ba su da mahanga.Ayyukkan kuɗin na haɗe tare da asalinku.
DeFi a buɗe ya ke ma kowa.Dole ku nema amfani da sabis na kuɗi.
Koyaushe kasuwan na a buɗe.Kasuwanin na rufewa ne don ma'aikatan na bukatar hutu.
Ana gina shi ne akan gaskiya - kowa na iya ganin bayanan kaya da kuma duba yadda tsarin ke aiki.Jami'o'in kuɗaɗe suna nan kamar rufaffen takarda ne: kuna iya tambayan su tarihin bashi, bayanan kadarorin da aka sarrafa, dama sauran su.
Gano manhajojin DeFi

Ya fara ne da Bitcoin...

Bitcoin a hanyoyi masu yawa shi ne farkon manhajar DeFi. Bitcoin na baku damar mallaka da sarrafa kima da kuma ganin shi a ko'ina a faɗin duniya. Yana haka ne ta samar da wani hanya wa mutane masu yawa, wanda ba su yarda da juna ba, da su amince da bayanai ajiyayyu na asusu ba tare da buƙatar wani amintacce a tsakiya ba. Bitcoin na buɗe ga kowa kuma ba wanda ke da ikon canza kowane doka. Dokokin Bitcoin, kamar dai yadda yake a buɗe kuma ba a cika samun sa ba, na rubuce a cikin fasiha. Ba kamar abubuwan da suka shafi kuɗi na da bane inda gwamnati ke buga kuɗi da ke rage darajar ajiyarku da kamfanoni har su kulle kasuwancin su.

Ethereum ita ma ta ɗaura ne akan wannan. Kamar dai Bitcoin, dokokin ba za su canza ba a kan ku ko kuma akan duk wanda ke da dama. Amma dai itama kuɗin dijital ne da aka tsara, ta amfani da , don ku iya wuce ma ƙarfin ajiya da kuma aika kuɗi.

Kuɗin da ake tsarawa

Wannan kun ji shi wani iri... ''Mesa zan so na tsara kuɗina''? Koda yake, wannan ya fi asalin yanayin siffar kuɗi ne akan Ethereum. Kowa zai iya tsara fikira har zuwa biyan kuɗi. Kuna iya samun damar sarrafawa da ma tsaro na Bitcoin da ke cakuɗe da sabis da kuka samar a cibiyar hada-hadar kuɗaɗe. Wannan na ba ku damar yin abubuwa da kuɗin kiripto da baza ku iya yi ba tare da Bitcoin kamar dai ba da aro da bashi, tsara jadawalin biyan kuɗi, saka hannun jarin kuɗi da ma sauran su.

Gano shawarwari na amfani da DeFi don gwadawa idan ku sabbi ne a Ethereum.
Gano manhajojin DeFi

Me za ku iya yi da DeFi?

Akwai hanyoyi da dama na madadin mafi yawan ayyukan hada-hadar kuɗi. Amma Ethereum kuma na ƙirƙirar damammaki da samun kayayyakin kuɗi da gabaɗaya sabbi ne. Wannan jeri ne dake kan girma har abada.

  • Tura kuɗi a duk faɗin duniya
  • Yi amfani da kudi a duk faɗin duniya
  • Samun kuɗaɗe masu ƙarfi
  • Nemi bashin kuɗi da jingina
  • Nemi bashi ba tare da jingina ba
  • Fara ajiyar kiripto
  • Kasuwancin kuɗin kiripto
  • Girmama kanku
  • Saka kuɗi kan shawarwarin ku
  • Siya inshora
  • Sarrafa kanku

Aika kuɗi a faɗin duniya cikin sauri

A matsayin blockchain, Ethereum an tsara shi ne don aika kuɗaɗe a gabaɗaya hanya cike da aminci. Kamar Bitcoin, Ethereum na aika kuɗi a ko'ina a cikin duniya cikin sauƙi kamar dai aika imel. Kawai ku higar da mai karɓa ( kamar bob.eth) ko kuma adireshin asusu daga walet ɗinku kuma kuɗin zai tasi kai tsaye zuwa gare su a cikin mintoci (kamar yadda aka saba). Don aika ko karbar kuɗi, za ku buƙaci walet.

Dubi dapps na biyan kuɗi

Yi amfani da kuɗi a faɗin duniya...

Za ku iya amfani da kuɗi a Ethereum. Wannan na sa ku iya biyan kuɗin albashi a sakonni, ba su damar samun kuɗin su a duk lokacin da suke buƙata. Ko kuma hayan wani abu a cikin sakonni kamar ma'ajiya a kulle ko abun hawa mai amfani da lantarki.

Kuma idan ba ku san aikawa ko amfani da saboda yadda darajar kuɗin ya canza, akwai wasu madadn kuɗade akan Ethereum: .

Samun kuɗaɗe masu ƙarfi

Kuɗin kiripto a gabaɗaya matsala ce ga kayayyakin kuɗi da ma kashe kuɗi na gabaɗaya. Al'ummar DeFi ta warware wannan matsalar da kuɗaɗe masu ƙarfi. Darajar su za su zama a manne da wani kadara, mafi yawanci kuɗin da ta fi shahara kamar daloli.

Tsilalla kamar Dai ko USDC suna da daraja da ke kasancewa a cikin ɗan wani sen ko dala. Wannan ne ya sa suka fi dacewa wajen samu ko dillanci. Mutane da yawa a Latin Amurka sun yi amfani da kuɗaɗe da basu rawa a matsayin wani hanya na ajiya a lokacin da ba a da tabbas kan kuɗin da gwamnati ta samar ake amfani da su.

Ƙari kan kuɗaɗen da ke da ƙarfi

Aro

Aron kuɗi daga masu samar da kuɗi na ko'ina na zuwa ne a hanyoyi guda biyu manya.

  • Mutum-zuwa-mutum, na nufin aron kuɗi kai tsaye daga masu bayar da bashi na musamman.
  • Daga cikin haɗaka inda masu bayar da kuɗi ke samar da kuɗaɗen (ruwa) zuwa haɗaka inda masu karɓar bashi za su iya ara daga wurin.
Dubi aron dapps

Akwai wasu amfanoni ta amfani da mas bayar da kuɗi na ko'ina...

Aron kuɗi cikin sirri

A yau, bayarwa da karɓar kuɗi na zagayuwa ne a cikin ɗaiɗaiku da ke cikin harkar. Bankuna na buƙatar sanin ko kuna son ku fara biyan bashin kafun ku bada aron sa.

Shi ba da bashi na ko'ina na aiki ne ba tare da wani ya kai ga bayyana kansa ba. A maimakon haka, mai karɓar bashin dole ne ya yi jingina da zai sa mai bayarwa zai samu atomatik idan bai biya ba. Wasu masu bada bashi na iya karɓar a matsayin jingina. NFTs suna nan a matsayin wata kadara ne na musamman, kamar zane. Ƙari akan NFTs

Wannan na baku damar karɓar bashin kuɗi ba tare da duba katin kuɗi ba ko kuma miƙa wasu bayanai na sirri.

Samun kuɗi a ko'ina cikin faɗin duniya

Idan kuka yi amfani da mai bada bashi na ko'ina kuna samun damar kuɗi na ko'ina daga ko'ina a cikin duniya, ba kawai kuɗin da ke tsakanen iyakar bankinku ba ko cibiya. Wannan na sa rance ya zaa an fi samu da kuma inganta kuɗin ruwa.

Sauƙin-haraji

Aran kuɗin na baku damar samun kuɗaɗen da kuke buƙata ba tare da siyar da ETH ɗinku ba (al'amari da za a iya sa haraji). A maimakon haka, kuna iya amfani da ETH a matsayin jingina wa bashin kuɗaɗe masu ƙarfi. Wannan na sa ku sami kuɗin da kuke buƙata na shiga kuma na barin ku ajiye ETH. Kuɗi masu ƙarfi sune kuɗaɗen da suka fi a lokacin da kuke buƙatar tsabar kuɗi domin darajar su baya rawa kamar dai ETH. Ƙari kan kuɗaɗen da ke da ƙarfi

Rance a walƙiya

Rancen walkiya sune tsigar da aka fi amfani da shi wajen masu bada bashi na ko'ina da kuke iya samun bashi ba tare da jingina ko kuma bayar da bayanan kai.

Ba a cika samu ba ga mutane maras amfani da fasaha a halin yanzu amma kuma yana iya samuwa ga kowa a rayuwa na nan gaba.

Yana aiki ne kan tushen da aka fitar da bashin kuma aka sake biya a yanayin aika kuɗi iri ɗaya. Idan ba za a biya ba, aika kudin na komawa ne kamar ba bataɓa yi ba.

Kuɗaɗe a ko yaushe ana riƙe su a siffar kuɗin haɗaka (babban haɗaka ne na kuɗaɗen da ake karɓar bashi). Idan ba a yi amfani da su ba a lokacin da aka bayar ba, wannan na kirkirar wani dama wa wani ya ari waɗannan kuɗin, gudanar da kasuwanci da su, da kuma biyansu a cike a lokaci guda kamar dai yadda aka are su.

Wannan na nufin dabaru da yawa za a iya amfani da su a hada-hadar kuɗi na bespoke. Misali mafi sauki shine wani na iya amfani da rancen flash don aran kuɗin har kamar kadarar wani farashi don su iya siyar da shi a wani musanya daban idan kuɗin ta fi sama.

A haka a cikin aika kudi guda, waɗannan na iya faruwa:

  • Ku ci bashi adadi X na $asset a $1.00 daga wurin musanya A
  • Kuna iya sayar da $asset ga musanya B a kan $1.10
  • Ku biya bashin ku don ku musanya da A
  • Za ku riƙe ribar ban da kuɗin da aka cire na hada hadar kuɗi

Idan musanya B darajar sa ya sauka haka kawai kuma mai asusun ya kasa siyan isasshe don biyan bashin farko, cinikin zai gaza ne kawai.

Don iya yin misalin da ke sama a cibiyar hada-hadar kuɗinmu na asali na duniya, kuna buƙatar kuɗaɗe masu yawa. Waɗannan tsalon yin kuɗi ana samun su ne kawai idan akwai wani kuɗi. Rance kamar walkiya misalai ne na zamanin da inda ba lallai sai ana da kuɗi za a sami kuɗi ba.

Ƙari akan rancen flash(opens in a new tab)

Fara ajiya da kiripto

Bayar da bashi

Kuna iya samu riba da kiriptonku ta wurin ba da rance kuma ku gani yadda kuɗin ku ke girma a lokaci. A halin yanzu riba ya fi wanda za ku samu a bankin ku (idan kun yi sa'a samun damar shiga daya). Ga nan misali a nan:

  • Kun bada aron Dai 100, kumakuɗi mai ƙarfi, zuwa abu kamar Aave.
  • Kuka sami Dai 100 (aDai) wanda kuɗi ne da ke wakiltar Dai da aka ranta.
  • aDai zai ƙaru ne bisa ga kuɗin ruwa da kuma ganin ragowar kuɗinku na ƙaruwa a walet. Dangane da shi, ragowar kuɗin walet ɗinku zai zama kamar 100.1234 bayan ƴan wasu kwanaki ko kuma awanni!
  • Kuna iya cire adadin luɗi na Dai da ya zo daidai da ragowar kuɗin aDai a kowane lokaci.
Duba rancen dapps

Ba-asara irin caca

Ba asarar caca kamar PoolTogether suna sa annashuwa da kuma sabbi hanyar fikira don ajiye kuɗi.

  • Ku siya tikit 100 ta amfani da kuɗin Dai 100.
  • Ku sami plDai 100 ta gabatar da tikitin ku guda 100.
  • Idan ɗaya daga cikin tikitin ku ya zama mai nasara, ragowar kuɗin plDai ɗinku zai ƙaru da kuɗin da aka ajje na kyauta.
  • Idan kuma baku yi nasara ba, plDai 100 ɗinku zai gangara gaba zuwa gasar mako na gaba.
  • Kuna iya cire kuɗin Dai na asali wanda ya ke daidai da ragowar kuɗin plDai a kowane lokaci.

Kuɗin da aka ajje na kyauta ana samun sa ne daga ribar kuɗin da aka ba da aro na kuɗin tiket kamar dai misalin da ke sama.

Gwada PoolTogether(opens in a new tab)

Musanya kuɗi

Akwai dubban kuɗaɗe a Ethereum. Musanyar ko'ina (DEXs) na baku damar kasuwancin kuɗaɗe daban-daban a duk lokacin da kuke so. Baku taɓa ba da damar sarrafa kadarorin ku. Wannan yana nan kamar amfani da musanya kudi a lokacin da aka ziyarci wata kasa daban. Amma shi tsigar DeFi ba a taɓa kulle shi. Kasuwar tana 24/7, kwanaki 365 a kowane shekara tare da garantin fasaha zai zama a koyaushe akwai wani da zai yi ciniki.

Alal misali, idan kuna son ku yi amfani da cacar da ba a hasara na PoolTogether (da aka kwatanta a sama), kuna buƙatar kuɗi kamar Dai ko USDC. Waɗannan DEXs ɗin na baku damar sauya ETH ɗinku zuwa waɗannan kuɗaɗen kuma ku sake mayarwa idan kuka gama.

Dubi musayar kuɗi

Ciniki na gaba

Akwai ƙarin zaɓuɓɓukan ci-gaba don yan kasuwa waɗanda suke son ɗan ƙaramin dama. Iyakance umarni, madawwama, cinikin gefe da ƙari duk mai yiwuwa ne. Tare da Karɓar ciniki za ku sami damar samun kuɗi na duniya, kasuwa ba ta rufewa, kuma koyaushe kuna iya sarrafa kadarorin ku.

Lokacin da kuke amfani da musayar waje dole ne ku saka kadararku kafin cinikin kuma ku amince da su don kula da su. Yayin da ake ajiyar kadarorin ku, suna cikin haɗari saboda kasuwancin da aka keɓance ta zama manufa mai kyau ga masu satar bayanai.

Duba ciniki dapps

Girmama kanku

Akwai samfuran sarrafa kuɗi akan Ethereum waɗanda za suyi ƙoƙarin haɓaka fayil ɗin ku bisa dabarun zaɓinku. Wannan atomatik ne, buɗe wa kowa, kuma baya buƙatar manajan ɗan'adam yana yanke ribar ku.

Kyakkyawan misali shine DeFi Pulse Index asusu (DPI)(opens in a new tab). Wannan asusu ne wanda ke sake daidaitawa ta atomatik don tabbatar da fayil ɗin ku koyaushe yana haɗe da manyan kuɗin DeFi ta hanyar babban kasuwa. Ba za ku taɓa sarrafa kowane bayanan ba kuma kuna iya janyewa daga asusun a duk lokacin da kuke so.

Duba zuba jari dapps

Saka kuɗi kan shawarwarin ku

Ethereum shine kyakkyawan dandamali don tara kuɗi:

  • Masu iya samun kuɗi na iya zuwa daga ko'ina - Ethereum da alamun sa suna buɗewa ga kowa, a ko'ina cikin duniya.
  • A bayyane yake don haka masu tara kuɗi za su iya tabbatar da adadin kuɗin da aka tara. Kuna iya gano yadda ake kashe kuɗi daga baya a hanya.
  • Masu tara kuɗi na iya saita maida kuɗi atomatik idan, alal misali, akwai takamaiman lokacin ƙarshe da ƙaramin adadin da bai cika ba.
Dubi taron haɗa kuɗin dapps

Tara kuɗi ta ɓangare huɗu

Manhajar Ethereum ce ta buɗe tushen kuma yawancin ayyukan da aka yi ya zuwa yanzu al'umma ne ke ba da kuɗi. Wannan ya haifar da haɓaka sabon samfurin tara kuɗi mai ban sha'awa: tara kuɗi ta ɓangare huɗu. Wannna yanada manufa wajen cigaban hanyoyi ki wani iri na abubuwan mutane anan gaba.

Kudin quadratic yana tabbatar da aiyuka dasuka karbi yawancin kudin sune kade abinda ake bukata. A wata maganan, aiyukan dasuka saya wajen inganta rayukan mafi yawan al'umma. Ga yadda abun ke aiki:

  1. Akwai madaidaicin haɗakar kuɗin da aka bayar.
  2. Ana fara zagaye na tallafin jama'a.
  3. Mutane na iya nuna buƙatarsu ta aikin ta hanyar ba da wasu kuɗi.
  4. Da zarar zagaye ya zo ƙarshe, ana rarraba haɗkar yadda ya dace da ayyukan. Waɗanda ke da buƙatu na musamman suna samun mafi girman adadin daga haɗakar kamar yadda ya dace.

Wannan na nufin Project A tare da gudummawar 100 na dala 1 zai iya ƙare tare da ƙarin kuɗaɗ fiye da Project B tare da gudummawa ɗaya na dala 10,000 (dangane da girman haɗakar da ya dace).

Ƙari akan tallafin kuɗi na ɓangare huɗu(opens in a new tab)

Inshora

Inshorar da aka raba ta da nufin sanya inshora ya zama mai rahusa, da sauri don biyan kuɗi, kuma mafi bayyane. Tare da ƙarin aiki na atomatik, ɗaukar hoto ya fi araha kuma biyan kuɗi yana yi cikin sauri. Bayanan da aka yi amfani da su don yanke shawara kan ikrarinku gabaɗaya ce.

Kayayyakin Ethereum, kamar kowace manhaja, na iya shan wahala daga matsaloli da amfani. Don haka a yanzu yawancin samfuran inshora a sararin wuri suna mayar da hankali kan kare masu asusu da su daga asarar kuɗi. Koyaya, akwai ayyukan da suka fara inganta ɗaukar hoto don duk abin da rayuwa za ta iya jefa mana. Kyakkyawan misali na wannan shine rufe Amfanin gona na Etherisc wanda ke nufin kare kananan manoma a Kenya daga fari da ambaliya(opens in a new tab). Inshorar da ba ta da tushe na iya ba da fa'ida mai rahusa ga manoma waɗanda galibi ana farashi daga inshorar cikin gida.

Duba inshora dapps

Masu tarawa da masu gudanar da fayil

Tare da ci gaba mai yawa, za ku buƙaci hanyar da za ku ci gaba da lura da duk jarin ku, lamuni, da kasuwancin ku. Akwai ɗimbin samfuran da ke ba ku damar daidaita duk ayyukan DeFi ɗinku daga wuri ɗaya. Wannan shine kyawun ginin gine-ginen DeFi. Ƙungiyoyi za su iya gina musaya inda ba za ku na iya ganin ma'aunan ku kawai a cikin samfuran ba, kuna iya amfani da fasalin su ma. Kuna iya samun wannan ya zama mai amfani kamar yadda kuke bincika ƙari cikin DeFi.

Duba fayil na dapps

Ta yaya DeFi ke aiki?

DeFi na amfani da kuɗin kiripto da kwangiloli masu fasaha don samar da ayyukan da ba sa buƙatar masu shiga tsakani. A cikin duniyar da ta ke na kuɗi ta yau, cibiyoyin kuɗi suna aiki a matsayin masu tabbatar da hada-hadar kuɗi. Wannan na ba wa waɗannan cibiyoyi iko mai yawa saboda kuɗin ku yana gudana ta cikin su. Haka kuma biliyoyin mutane a duniya ba za su iya samun asusun banki ba.

A cikin DeFi, kwangila na fasaha ya maye gurbin cibiyar kuɗi a cikin kasuwanci. Kwangilar fasaha na wani nau'in asusun Ethereum ne wanda zai iya ɗaukar kuɗi kuma zai iya aikawa/mayar da su bisa wasu sharuɗɗa. Babu wanda zai iya canza wannan kwangilar fasahar a lokacin da yake aiki- koyaushe zai gudana kamar yadda aka tsara.

Ana iya tsara kwangilar don bayar da alawus ko kuɗin aljihu ko kuma aika kuɗi daga Account A zuwa Account B kowace Juma'a. Kuma zai na yin hakan ne kawai muddin Account A yana da kuɗin da ake buƙata. Babu wanda zai iya canza kwangilar da ya ƙara Account C a matsayin mai karɓa don satar kuɗi.

Kwangilolin kuma na jama'a ne don kowa ya duba ya gyara. Wannan yana nufin kwangiloli marasa kyau sau da yawa za su zo ƙarƙashin binciken al'umma da sauri.

Wannan yana nufin a halin yanzu akwai buƙatar amincewa da ƙarin membobin masu ilimin fasaha na al'ummar Ethereum waɗanda za su iya karanta lambar. Buɗe tushen al'umma yana taimakawa wajen kiyaye masu ƙirƙira, amma wannan buƙatar za ta ragu cikin lokaci yayin da kwangilar wayo ta zama mafi sauƙi don karantawa da sauran hanyoyin tabbatar da amincin lambar.

Ethereum da DeFi

Ethereum shine cikakken tushen DeFi saboda dalilai da yawa:

  • Babu wanda ke da Ethereum ko kwangilolin fasaha da ke aiki a kai - wannan yana ba kowa damar amfani da DeFi. Wannan kuma yana nufin babu wanda zai iya canza dokoki akan ku.
  • Kayayyakin DeFi duk suna magana da harshe iri ɗaya a bayan fage: Ethereum. Wannan yana nufin yawancin kaya suna aiki tare ba tare da matsala ba. Kuna iya ba da lamuni akan dandali ɗaya kuma ku musanya alamar sha'awa a cikin wata kasuwa daban akan amfani daban. Wannan yana kama da samun damar kuɗin yarda da bankin ku.
  • Alamu kuɗin kiripto an gina su a cikin Ethereum, jagorar da aka raba - kiyaye hada-hadar kuɗi da mallakar wani abu ne na Ethereum.
  • Ethereum na ba da cikakken 'yanci na kuɗi - yawancin samfuran ba za su taɓa ɗaukar kuɗin ku ba, suna barin ku cikin iko.

Kuna iya tunanin DeFi a cikin wurare:

  1. Blockchain - Ethereum tarihin hada-hadar kuɗi ne da matsayin asusun.
  2. Kadarorin – ETH da sauran kuɗaɗe (kuɗi).
  3. Ka'idojin - waɗanda ke ba da ayyuka, alal misali, sabis ɗin da ke ba da izinin rarraba rancen kadarorin.
  4. Aika da su - samfuran da muke amfani da su don sarrafawa da samun damar ƙa'idodin.

Bayanan kula: yawancin DeFi suna amfani da . Amfani a cikin DeFi suna amfani da nannaɗuwa don ETH da ake kira Wrapped Ether (WETH). Ƙara koyo game da nannaɗe ether.

Gina DeFi

DeFi tafiya ne na buɗaɗɗen tushe. Ka'idojin DeFi da aiki da su duk a buɗe suke don ku bincika, fork, da ƙirƙira su. Saboda wannan tari mai ɗorewa (dukkansu suna raba tushe guda ɗaya da kadarori), ana iya haɗa ƙa'idodi kuma a daidaita su don buɗe damar haɗuwa ta musamman.

Ƙari kan gina dapps

Karatu na gaba

Bayanan DeFi

Muƙalun DeFi

Videos

Al'ummomi

Wannan shafin ya taimaka?