Tsallaka zuwa babban shafi
Sami hoton jarumin ETH

Inda za'a samu ETH

Kuna iya samun ETH, samun shi daga takwarorinku, ko saya shi daga musayar da manhaja.


Farashin ETH na yanzu (USD)

Yana lodin...
(Awa 24 da ta wuce)
Nema da ƙasa

Cinikayya na gabaɗaya

Musayar wasu kasuwanci ne da suke hanya da za ku siya kiripto da kuɗi. Suna da dama akan ko wane irin ETH da ka siya har sai ka turo zuwa walet da take ƙarƙahin ikon ka.

Sami ETH

Kuna iya samun ETH ta hanyar aiki don DAOs ko kamfanonin da ke biyan kuɗi a cikin kiripto, cin nasarar samun kyauta, gano matsala na cikin manhaja da sauran su.

Samu ETH daga abokan hulɗa

Da zarar kuna samu asusun Ethereum, duk abin da kuke buƙatar yi shi ne raba adireshinku don fara aikawa da karɓar ETH (da sauran alamun) a tsakanin takwarorinsu.

Cinikayya da ke cin gashin kansu (DEXs)

Idan kuna son karin iko, saya ETH ta amfani da . Ta DEX za ku iya kasuwanci da kadarorin dijital ba tare da taba ba da ikon sarrafa kuɗin ku ga kamfani na tsakiya ba.

Wallets

Wasu walet ɗin suna ba ku damar siyan kiripto tare da katin zare kuɗi/kiredit, canja wurin banki ko ma Apple Pay. Ana amfani da iyaƙancewa na yanki.

Kyautar adana

In dama kuna da wasu ETH, za ku iya samun ƙari ta hanyar gudanar da node na tabbatarwa. Za a biya ku don yin wannan aikin tabbatarwa a cikin ETH.

Duk kayayyakin da aka jera akan wannan shafin babu amincewar hukuma, kuma an samar dasu don dalilai na bayanai ne kawai. Idan kuna son ƙara kayan ko bayar da ra'ayi kan manufofin, ku shigar da batun a GitHub. Ɗaga matsala(opens in a new tab)

A wane ƙasa kake da zama?

Musayar suna da iyaƙa akan inda zasu iya siyar da kiripto. Wannan jerin bayanai ne na ayyukan da ake zaton za su yi aiki a kowace kasa. Mahadi a nan ba tallafi bane—ya kamata ku yi binciken kanku!

Shigar da wurin da kake zama...

Shigar da ƙasar da kake zaune don ganin jerin musayar da za ka iya amfani da su

Cinikayya da ke cin gashin kansu (DEXs)

Mene DEXs?

Musanyar ko'ina ta buɗede kasuwanni ne don ETH da sauran kuɗi. Suna haɗa masu siye da masu siyarwa kai tsaye.

Maimakon amfani da amintaccen ɓangaren uku don kiyaye kuɗi a cikin cinikayya, suna amfani da lamba. Za a canza wurin ETH na mai siyarwa lokacin da aka tabbatar da biyan kuɗi. An san wannan nau'in lambar a matsayin smart contracts. Ƙarin bayani game da smart contracts

Wannan yana nufin cewa akwai ƙarancin nauo'in zaɓuka a wannan sashen. Idan akwai wanda zai sayar maka da wani haja kuma zai gamsu da duk nau'in biyan da za ka yi masa, za ku samu dacewa.

Za ka buƙaci walet domin amfani da DEX.

Samu walet

Siya da kuɗaɗen kiripto

Musanya kuɗinku don ETH na wasu mutane. Da kuma akasin haka.

Ajiye ETH ɗinka cikin tsaro

Wallafawar al'umma akan tsaro

Babu wata hukuma mai kula da gudanar da Ethereum - ita ce ke cin gashin kanta.

Wannan yana nufin kana bukatar ka ɗauki tsaro da kuɗi da muhimmanci. Tare da ETH, ba ka amincewa da banki ko kamfani don kula da dukiyarka, kana ɗaukar kua da kanka.

Ajiye ETH ɗinka a walet

Ɗaya daga cikin manyan fasalulluka na Ethereum shine ku ci gaba da sarrafa dukiyar ku ta hanyar sarrafa asusun ku. Wannan yana nufin ba lallai ne ka amince da wani bangare na uku da kadarorinka ba, kuma ana kiyaye ka daga duk wani ma'aikacin da ke yin rashin gaskiya, yin fatara ko yin kutse. Koyaya, hakan yana nufin ku ɗauki alhakin tsaron ku.

Duba walet

Adireshin ETH ɗinka

I dan kuka sauke walet zai samar muku da adireshin ETH na jama'a. Ga yadda yake:

0x0125e2478d69eXaMpLe81766fef5c120d30fb53f

Misali: Kar a kwafa

Ka ɗauki wannan kamar adireshin imel ɗinka, amma maimakon wasiku zai na karɓar ETH. Idan kana son canza wurin ETH daga musayar zuwa walet ɗinka, yi amfani da adireshinka a matsayin wurin zuwa. Ka tabbata ka duba sau biyu kafin ka aika!

Bi dokokin walet

Idan kun rasa damar shiga asusunku, za ku rasa kuɗin ku. Walat din ku ya kamata ya ba ku umarni kan ƙariya daga wannan. Tabbatar kun bi su cike da kulawa—a mafi yawan lokuta, babu wanda zai iya taimaka muku idan kun rasa damar shiga asusunku.

Wannan shafin ya taimaka?