Menene NFTs?
NFTs kadarori ne na musamman ga kowane mai amfani. Kowani NFT na da kayayyaki daban-daban (mara ƙarfi) sannan sukan yi wahalar samu. Wannan shine bambancin da ke tsakanin tokens irin su ko wasu Ethereum dasuka danganci tokens kamar USD alhalin kowani token suna kamanceceniya da juna kuma suna da yanayi iri ɗaya ('mai ƙarfi'). Baka damu da buƙatan da wata kalar kuɗi na dala (ko ETH) yake cikin lalitar ka ta ajiya, saboda dukkannin su daya ne basu da banbanci. Kodayake, kai aiwatar da kulawa na NFT na musamman wanda ka mallaka, sabida kowannen naɗa yanayinshi na musamman da banbance su da sauran da ('basu da ƙarfi').
Ko keɓanta da NFT keɗai shi na sanya alama na ababe kamar zane, ababen da aka tara, ko gini wato (real estate), tayadda kowane NFT ke wakiltan wasu ababen da suke a bayyane ko na dijital. Mallakar kadara ana tantancewa na game gari akan Ethereum .
Wannan kadarar shafin intanet ne
NFTs da Ethereum sun magance wasu daga cikin matsaloli da ska wanzu a yanar gizo a yau. Kamar yadda aka zamanartar da komai ya zamto dijital, akwai bukatuwar canza ababen da suke bayyane kamar abu mai wuyan samu, da ababen da kama da juna, da tantance abunda aka mallaka ta yadda ƙungiya wato (central organization) bazasu iya sarrafasu ba. Misali, da NFTs, zaku iya samu fayil na waƙan/sautin mp3 daga kundin Ethereum wanda bazaku taɓa samu a kundin wata kamfani ba irin waƙokin Spotify ko Apple. Kuna iya mallakr kafafen sadarwan da zaku iya sayarwa or musanyawa, amman wa'inda suka samar da kudin na iya amshewa daga gareku ba bisa ƙa'ida ba .
A nan ne yadda yanar gizon NTFs ke daidaituwa zuwa yanar gizo ta yadda dayawan mu ke amfan8 dashi a yau...
Kwatantawa
Yanar gizon NFT | Yanar gizon mu a yau |
---|---|
Kuna iya mallakar kadararku! Kawai in zaku seyar koku musanya su. | Kun hayi kadara daga wasu ƙungiyoyi amman suna iya amshewa daga gurinku. |
NFTs sune keɓanatattu na dijital, babu NFTs iri ɗaya. | Ba a iya bambance kwafi daga na asali. |
Dukan abun da aka mallaka na NFT an killace shi a blockchain domin tantance kowa. | Samun damar yin amfani da bayanai na ababen dijital ana sarrafasu ne daga cibiyoyin da wajibi ne ku bi kudurinsu. |
NFTs sune akan Ethereum. Hakan na nufin suna da damar yin aiki a wasu ɓangaren da suka shafi kwangila da manhajoji na Ethereu! | Kamfanonin da suka mallaka kayan dijital suna buƙatar mallakar "ganuwa" da kayan aiki. |
Masu Kirkiran bayanan na ciki suna iya sayar da ayyukansu a ko ina sannan suna da lko akan kasuwan duniya. | Masu ƙirkiran kundi na bakin ƙokarinsu wajen samar da kayan aiki da tafiyar da ababen da suke amfani dasu. Wannan sune ababen da sukafi shara na tsarin amfani da dokokin yanki. |
Masu ƙirkƙiran NFTna da damar mallakar ƴanci akan aiykansu, sannan da jadawalin mai matsayi kai tsaye zuwa ga kwangilar NFT. | Dandamalai, irin aiyukan yawi, sun rike mafiyawacin riba daga masu sayerwa. |
Akan me ake amfani da NFTs?
NFTs ana amfani dasu akan ababe da yawa, sun haɗa da:
- tabbatar da cewa ka halarci taron
- shaidar tabbacin cewa ka kammala darasi
- samun damar mallakar dukkanin ababen da danganci wasanni
- zanen dijital
- sanya alama akan dukkan kadarori na zahiri
- samar da bayanan asali na kan intanet
- samun damar shiga ƙunshin
- bayar da tikiti
- rarraba sunayen domain na yanar gizo
- jingina a
Ta iya yuwa kai mai zane ne mai so ya raba aiyukansa ta hanyar amfani da NFTs, ba tare da ka rasa iko ba da sadaukar da ribar ka ga yantsakiya ba. Kana iya ƙiƙiran sabon kwangila tare keɓance lambar NFTs, kayayyaki da matsomi zuwa ga wasu aikin fasaha na musammanma. A matsayin mai zane, kana iya shiryawa don shiga smart contract don samun ɗaukaka wajibine sai ka biya (e.g tura 5% na farashin duk NFT daka sayar zuwaga dan kwangila). Sannan kuma ko wane lokaci kana iya tabbatar da cewa ka ƙirkiri NFTs saboda ka mallaki dake wanzar da kwangilar. Masu siyan na ku cikin sauƙi na iya tabbatar da cewa sun mallaki sahihancin NFT daga tarin ku saboda ana haɗe tare da alama a cikin smart contract. Za su iya amfani da shi a duk faɗin tsarin mahallin Ethereum, suna da tabbaci akan sahihancinsa.
Ko kuma ka mayar da hankali kan tikiti game da taron wasannin. Kamar dai a matsayin ka na na mai shirya taro kana iya zaban yawan tikitin da zai sayar, mai kirkiran NFT zai iya yanke hukuncin adadin kwafin da suke akwaisu. Wasu lokutan waɗannan sune asalin kwafin, kamar 5000 Amintattun Tikiti na Game Gari. Wasu lokutan dayawa suna buga wainda suka fi kama, amman sunada dan banbanci kaɗan, kamar irin tikitan da aka sama musu wuri. Wa'innan ana iya yi kuma a sayar dasu hannu da hannu ba tareda biyan masu tikitin ba sanna masu siye koda yaushe sunada tabbacin ingacin tikitin ta hanyar duba adreshin kwangilar.
A Ethereum.irg, NFTs ana amfani da su ne wajen nunawa a al'ummah yadda zasu bayar da gudunmawa mai ma'ana ga ma'ajiyin Github (tsara shafin yanar gizo, rubuta ko inganta maƙalai....), fassara aiyukanmu, ko amsa kira al'ummarmu, sannan mun mallaki sunan domain na NFT. Idan ka bada gudunmowa a ethereum.org, kana iya samun a NFT. Wasu daga cikin taron da aka gudanar na kiripto sunyi amfani da PIAPs a matsayin tikiti. Mafi yawa akan ba da gudunmawa.
Wannan shafin intanet shima yana da sunan domain don maye gurbi wanda NFTs suka ɗauki nauyi, Ethereum.eth. Areshinmu na .org
ana kula dashi daga masu samar da domain name system (DNS), shi kuma ethereum.eth
anyi mishi rajista da Ethereum ta Ethereum Name Service (ENS). Sannan mun mallakesu sannan mu ke kula dasu. Duba namu matattarar ENS(opens in a new tab)
Ƙari akan ENS(opens in a new tab)
Ya NFTs suke aiki?
NFTs, kamar yadda ababen dijital suke a Ethereum blockchain, na ƙirƙiresu ne ta hanayar tsari na komfuta da ya danaganci Ethereum da aka musu laƙabi da "smart contract". Wa'innan kwangilar sun bi dokokin da aka gindaya, kamar ko yadda ake yi, wanda hakan ke nuna abunda kwangilar zai iya yi.
Smart contracts NFT na yin abubuwa kamar haka:
- Ƙirƙiran NFTs: Na iya yin sabon NFTs.
- Sanya Mallaka: Shi ke adanan bayanen waye mamallakin NFTs ta hanya sadar dashi zuwa ga adreshin Ethereum na musamman.
- Baiwa Kowani NFT shaida ta musamman: kowani NFT nada wata lamba da yasa ya bambanta. Bugu da ƙari, akwai mafi yawancin bayanai (metadata) da aka haɗa da shi, dake bayani akan abinda NFT ke wakilta.
Idan wani ya "kirkiri" ko "samar" da NFT, suna sanar da smart contract akan ya basu damar mallakar wani sashen NFT. Wannan bayanin an tsare su sannan an adana su a blockchain.
Bugu da ƙari, mai kirkirar kwangilar zai iya ƙara wasu dokoki daban. Za su iya taƙaita adadin NFT da za su iya ƙirƙira ko Yanke hukunci don samar da ƙaramin haraji a kowani lokacin da akayi wani canji a NFT.
Tsaron NFT
Cikakken tsaron da Ethereum ke samu yana zuwa ne daga . Shi tsarin an zana shi ne domin raunata tattalin arzikin aiki mare kyau, domin inganta tsaron Ethereum na ƙare shi daga kutse a cikin shi. Wannan shine dalilin da yasa NFT ya zamto mai yuwa. Da zarar an da NFT na hada-hada kuɗinka zai kai ga sannan zai kawo wa mai kai hari asarar miliyoyn Ethereum don janza shi. Duk wanda ke amfani da manhajan Ethereum kai tasye za a dakatar da shi daga damar kutse cikin NFT, sannan mai kokarin aikata hakan zai fuskanci hukunci ta hanyar dakatar da shi.
Dukkan abu da ya shafi matsala ta tsaro da NFTs suna yawan kamanceceniya da matsalar mayaudara, smart contracts da matsalar da mutum ke samu (bayyana bayanan sirri), sannan tsare lalita da tsaro mai kyau don mamallakan NFT.
Ƙari kan tsaroKaratu na gaba
- Jagorar NFT gan masu koya(opens in a new tab) – Linda Xie, Janairu 2020
- Mai bibiyar EtherscanNFT(opens in a new tab)
- ERC-721 tsarin kuɗi
- ERC-1155 tsarin kuɗi
- Mafi shaharar kuɗin NFT da kayan aiki(opens in a new tab)